Muhammadu Maccido

Muhammadu Maccido
Sultan na Sokoto

20 ga Afirilu, 1996 - 29 Oktoba 2006
Ibrahim Dasuki - Sa'adu Abubakar
Rayuwa
Haihuwa Dange Shuni, 20 ga Afirilu, 1926
ƙasa Najeriya
Mutuwa Abuja, 29 Oktoba 2006
Yanayin mutuwa accidental death (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Siddiq Abubakar III
Sana'a
Sana'a sarki

Ibrahim Muhammadu Maccido ɗan Abubakar, (Haihuwa: 20 ga watan Afrilu shekarar 1928 Rasuwa: 29 ga watan Oktobar shekarar 2006), wanda aka fi sani da Muhammadu Maccido, shi ne Sarkin Musulmi na 19 a kasar nigeria . Ya kuma kasance mataimaki na farko ga Siddiq Abubakar III (shekarar 1903–shekarar 1988) wanda ya kasance Sarkin Musulmi na tsawon shekaru 50. Maccido ya yi ayyuka da dama, na gwamnati a lokacin rayuwarsa kuma ya yi fice sosai a matsayin mai hulda da Shugaban kasar Nijeriya Shehu Shagari (mulki shekarar 1979 – shekarar 1983) har zuwa lokacin da sojoji suka yi juyin mulki suka kawar da Shagari daga mulki. Lokacin da mahaifinsa ya mutu a shekarar 1988, shugaban gwamnatin mulkin soji a Najeriya, Ibrahim Babangida ya nada Ibrahim Dasuki (mulki a shekarar 1985 – shekarar 1993) a matsayin sabon Sarkin Musulmi, shawarar da ta haifar da zanga-zanga mai ƙarfi a duk arewacin Nijeriya.

A shekarar 1996, Sani Abacha (shekarar 1993 – shekarar 1998), tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya 6, ya tumɓuke Dasuki daga muƙaminsa ya kuma naɗa Maccido sabon Sarkin Musulmi. An kuma naɗa Maccido a ranar 21 ga watan Afrilu shekarar 1996 kuma ya yi mulki daga matsayin na tsawon shekaru goma. Ya kuma yi amfani da mukamin don kokarin sasanta rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Musulmin arewacin Najeriya, da inganta alaka da sauran al’ummomin Musulmi, da rage rikice-rikicen kabilanci a cikin Najeriya. A ranar 29 ga watan Oktoba shekarar 2006, bayan ganawa da Shugaba Olusegun Obasanjo, Maccido ya mutu a hatsarin jirgin saman kamfanin jirgin sama na ADC Airlines Flight 53, tare da ɗansa Badamasi Maccido, yayin da suke komawa Sakkwato. Akuma n binne shi a Sakkwato tare da yawancin sauran Sarakunan na Sakkwato.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy